Amos 9:14 - Sabon Rai Don Kowa 202014 Zan dawo da waɗanda aka kai zaman bauta mutanena Isra’ila. “Za su sāke gina biranen da suke kango su kuma zauna a cikinsu. Za su shuka gonakin inabi su kuma sha ruwan inabinsu; za su yi lambuna su kuma ci amfaninsu. အခန်းကိုကြည့်ပါ။Littafi Mai Tsarki14 Zan komo da mutanena ƙasarsu, Za su giggina biranensu da suka rurrushe, Su zauna a cikinsu. Za su shuka gonakin inabi, su sha ruwan inabin. Za su yi lambuna, su ci amfaninsu. အခန်းကိုကြည့်ပါ။ |
sowa ta farin ciki da murna, muryoyin amarya da na ango, da muryoyin waɗanda suka kawo hadayun salama a gidan Ubangiji suna cewa, “ ‘ “Ku yi godiya ga Ubangiji Maɗaukaki, gama Ubangiji mai alheri ne; ƙaunarsa za tă dawwama har abada.” Gama zan mayar da wadatar ƙasar kamar yadda suke a dā,’ in ji Ubangiji.