Amos 5:12 - Sabon Rai Don Kowa 202012 Gama na san yawan laifofinku da kuma girman zunubanku. Kuna danne masu adalci kuna kuma cin hanci kuna kuma hana a yi wa matalauta shari’ar adalci a majalisa. အခန်းကိုကြည့်ပါ။Littafi Mai Tsarki12 Na san irin zunuban da kuke yi, Da mugayen laifofin da kuka aikata. Kuna wulakanta mutanen kirki, Kuna cin hanci, Kuna hana a yi wa talakawa shari'ar adalci a majalisa. အခန်းကိုကြည့်ပါ။ |
“Ta haka zan zo kusa da ku don in yi hukunci. Zan hanzarta ba da shaida a kan masu yin sihiri, da mazinata da masu shaidar zur. Zan ba da shaida a kan waɗanda suke zaluntar ma’aikata a kan albashinsu, da waɗanda suke ƙwarar gwauraye da marayu, suna kuma hana baƙi samun adalci, ba sa ma tsorona,” in ji Ubangiji Maɗaukaki.