waɗanda ta magana kawai sukan mai da mutum mai laifi, waɗanda suke kafa tarko wa mai ba da kāriya a ɗakin shari’a da shaidar ƙarya kuma su hana marar laifi samun shari’ar adalci.
Sarkin Isra’ila ya amsa wa Yehoshafat, ya ce, “Akwai mutum guda har yanzu wanda ta wurinsa za mu iya nemi nufin Ubangiji, amma na ƙi jininsa domin bai taɓa yin annabci wani abu mai kyau game da ni ba, sai dai mummuna kullum. Shi ne Mikahiya ɗan Imla.” Yehoshafat ya ce, “Kada sarki ya ce haka.”
Amma suka yi wa ’yan saƙon Allah ba’a, suka rena maganarsa, suka yi wa annabawansa dariyar reni, har sai da fushin Ubangiji ya tasar a kan mutanensa babu makawa.
Tun yana cikin magana, sai sarki ya ce masa, “Yaushe muka naɗa ka mai ba sarki shawara? Rufe mana baki! Me zai hana a kashe ka?” Sai annabin ya yi shiru, amma ya ce, “Na dai sani Allah ya riga ya shirya zai hallaka ka, saboda ka aikata wannan, ba ka kuma saurari shawarata ba.”