Zan yi kuka in yi kururuwa saboda duwatsu in kuma yi makoki game da wuraren kiwon hamada. Sun zama kango ba wanda yake bi cikinta, ba a kuma jin kukan shanu. Tsuntsaye sararin sama sun gudu namun jeji ma duk sun watse.
A wannan rana mutane za su yi muku ba’a za su yi muku gwalo da wannan waƙar makoki, ‘An lalatar da mu sarai; an rarraba mallakar mutanena. Ya ɗauke shi daga gare ni! Ya miƙa filayenmu ga maciyan amanarmu.’ ”
Saboda haka ga abin da Ubangiji, Ubangiji Allah Maɗaukaki yana cewa, “Za a yi kururuwa a dukan tituna a kuma yi kuka don azaba a dukan wuraren da jama’a sukan taru. Za a yi kira ga manoma su yi kuka masu makoki kuma su yi kuka.
Ku kasa kunne ga wannan, ya ku shanun Bashan a kan Dutsen Samariya, ku matan da kuke cin zalin matalauta, kuke kuma danne matalauta, kuna kuma ce wa mazanku, “Ku kawo mana abin sha!”
“Ɗan mutum, ka yi makoki a kan Fir’auna sarkin Masar ka faɗa masa. “ ‘Kai kamar zaki ne a cikin al’ummai; kai kamar dodon ruwa a cikin tekuna kana ɓullowa cikin rafuffukanka, kana gurɓata ruwa da ƙafafunka kana kuma dama rafuffuka.
“Ɗan mutum, ka yi makoki domin sarkin Taya ka kuma ce masa, ‘Ga abin da Ubangiji Mai Iko Duka yana cewa, “ ‘Ka kasance hatimin cikakke, cike da hikima da cikakke a kyau.
Sa’an nan za su yi makoki game da ke su ce, “ ‘Yaya kika hallaka haka nan, ya birnin da ta yi suna, cike da mutanen teku! Ke da kika zama mai ƙarfi cikin tekuna, ke da mazauna cikinki; kin sa tsoronki a kan dukan waɗanda suka zauna a can.
Wuta ta fito daga jikin rassanta ta cinye ’ya’yanta. Babu sauran reshe mai ƙarfin da ya rage a kanta da ya dace da sandar mai mulki.’ Wannan waƙa ce kuma za a yi amfani da ita a matsayin makoki.”
Saboda haka ga abin da Ubangiji yana cewa, “Ku tattambaya a cikin al’ummai. Wa ya taɓa jin irin wannan abu? Budurwa Isra’ila ta yi mugun abu mafi banƙyama.
Waɗanda suka yi rantsuwa da abin kunya na Samariya, ko kuma su ce, ‘Muddin allahnku yana a raye, ya Dan,’ ko kuwa, ‘Muddin allahn Beyersheba yana a raye,’ za su fāɗi, ba kuwa za su ƙara tashi ba.”