Amos 3:14 - Sabon Rai Don Kowa 202014 “A ranar da zan hukunta Isra’ila saboda zunubanta, zan hallaka bagadan Betel; za a yayyanka ƙahonin bagadan za su fāɗa ƙasa အခန်းကိုကြည့်ပါ။Littafi Mai Tsarki14 “Ran da na hukunta mutanen Isra'ila saboda zunubansu, Zan hallakar da bagadan Betel. Za a kakkarya zankayen bagaden, Su fāɗi ƙasa. အခန်းကိုကြည့်ပါ။ |
Sa’ad da aka gama dukan wannan, sai Isra’ilawan da suke can suka fita zuwa garuruwan Yahuda, suka rurrushe keɓaɓɓun duwatsu suka kuma farfashe ginshiƙan Ashera. Suka rurrushe masujadan kan tudu da bagadai, ko’ina a Yahuda da Benyamin da kuma cikin Efraim da Manasse. Bayan sun rurrushe dukansu, sai Isra’ilawa suka koma garuruwansu, kowanne zuwa mahallinsa.