Ka ba da girma ga mahaifinka da mahaifiyarka, yadda Ubangiji Allahnka ya umarce ka, don ka yi tsawon rai, ka kuma sami zaman lafiya a ƙasar da Ubangiji Allahnka yake ba ka.
Ku kiyaye ƙa’idodi da umarnai, waɗanda nake ba ku a yau, domin zaman lafiyarku da kuma na zuriyarku bayan ba ku, domin kuma ku yi tsawon rai a ƙasa wadda Ubangiji Allahnku yake ba ku har abada.
Ku yi hankali, ku yi biyayya da dukan waɗannan umarnan da nake ba ku, da kuma ’ya’yanku, don ku zauna lafiya, da ku da ’ya’yanku a bayanku, gama za ku riƙa aikata abin da yake daidai da kuma yake mai kyau a gaban Ubangiji Allahnku.
Ku ji, ya Isra’ila, ku kuma kula, ku kiyaye su don yă zama muku da lafiya, ku kuma ƙaru sosai a ƙasa mai zub da madara da zuma, kamar dai yadda Ubangiji, Allahn kakanninku ya yi muku alkawari.
Ko ya gamshe mu ko bai gamshe mu ba, za mu yi biyayya da Ubangiji Allahnmu, ga wanda muke aikan ka, saboda ya zama mana da amfani, gama za mu yi biyayya da Ubangiji Allahnmu.”
Ku aikata abin da yake daidai da kuma mai kyau a idon Ubangiji, don yă zama muka da lafiya, ku kuwa shiga ku mallaki ƙasa mai kyau da Ubangiji ya yi alkawari da rantsuwa ga kakanninku.
Haka kuma ba za ku gina gidaje, ku dasa iri ko ku nome gonakin inabi ba; kada ku kasance da wani daga cikin waɗannan abubuwa, amma dole kullum ku zauna a tentuna. Ta haka za ku yi dogon rai a cikin ƙasar baƙuncinku.’