Amma ina gaya muku, duk wanda ya yi fushi da ɗan’uwansa, za a hukunta shi. Kuma duk wanda ya ce wa ɗan’uwansa ‘Raka,’ za a kai shi gaban Majalisa. Amma duk wanda ya ce, ‘Kai wawa!’ Zai kasance a hatsarin shiga jahannama ta wuta.
Sai ya kalle su da fushi, don taurin zuciyarsu ya ɓata masa rai sosai. Sai ya ce wa mutumin, “Miƙo hannunka.” Sai ya miƙa, hannunsa kuwa ya koma lafiyayye.
Dukan fadawan nan naka za su zo wurina, suna fāɗi a gabana suna cewa, ‘Ka fita, kai da dukan jama’arka!’ Sa’an nan zan fita.” Daga nan sai Musa ya fita daga gaban Fir’auna a husace.
Ku biya kuɗin aikinsa kowace rana kafin fāɗuwar rana, domin shi matalauci ne, yana kuma sa rai a kan wannan hakkin ne, don kada ya yi wa Ubangiji kuka a kanku, har yă zama laifi a gare ku.
Yonatan ya tashi daga tebur cin abincin da fushi. A rana ta biyun kuwa bai ci abinci ba, gama yana baƙin ciki game da rashin kunyar mahaifinsa game da Dawuda.