Kada ku ci gaba da yin abin da duniya take yi, sai dai ku bar halinku ya sāke, ta wurin sabunta hankalinku ɗungum, don ku tabbatar da abin da Allah yake so yake, abu mai kyau, mai daɗi da kuma cikakke.
sai ya cece mu, ba saboda abubuwan adalcin da muka aikata ba, sai dai saboda jinƙansa. Ya cece mu ta wurin wankan nan na sāke haihuwa da kuma sabuntawan nan ta Ruhu Mai Tsarki,
Saboda haka, an binne mu da shi ke nan, ta wurin baftisma cikin mutuwarsa, domin kamar yadda aka tā da Kiristi daga matattu ta wurin ɗaukakar Uba, haka mu ma mu yi zaman sabuwar rayuwa.