Yanzu, ina farin ciki saboda wuyar da nake sha dominku, don ta wurin wuyan nan zan cika abin da ya rage na wuyar da Kiristi ya sha saboda jikinsa, wato, ikkilisiya.
A wannan sabuwar rayuwa babu bambanci ko kai mutumin Al’ummai ne ko mutumin Yahuda, mai kaciya ne ko marar kaciya, baƙo, baƙauye, bawa ne ko ’yantacce, gama Kiristi shi ne kome, kuma yana cikin kome.
Wannan zai ci gaba har sai mun zama ɗaya a cikin bangaskiya da kuma ta wurin fahimtarmu na Ɗan Allah. Sa’an nan za mu zama balagaggu, kamar yadda Kiristi yake, mu kuma zama gaba ɗaya cikakku kamar sa.
Ya yanke dangantaka da Kiristi wanda yake kai, wanda ta gare shi ne dukan jiki yake a haɗe, yake tsaye ta wurin taimakon gaɓoɓi da jijiyoyi, yana kuma girma kamar yadda Allah yake sa yă yi girma.