Ba mu bi tatsuniyoyin da aka ƙaga da wayo sa’ad da muka gaya muku game da ikon Ubangijinmu Yesu Kiristi da zuwansa ba, sai dai mu shaidu ne na ɗaukakarsa mai girma da muka gani da ido.
Timoti, ka lura da abin da aka danƙa maka amana. Ka yi nesa da masu maganganun rashin tsoron Allah da kuma yawan mūsu da ake ƙarya, ake ce da shi ilimi,
Sukan ce wa masu gani, “Kada ku ƙara ganin wahayi!” Ga annabawa kuwa sukan ce, “Kada ku ƙara ba mu wahayin abin da yake daidai! Faɗa mana abubuwan da muke so mu ji ne kawai, ku yi annabcin abin da zai ruɗe mu.
Gama zuciyar mutanen nan ta taurare; da ƙyar suke ji da kunnuwansu, sun kuma rufe idanunsu. Da ba haka ba, mai yiwuwa su gani da idanunsu, su kuma ji da kunnuwansu, su gane a zuciyarsu, su kuwa juya, in kuma warkar da su.’