17 A maimakon haka ma, sa’ad da yake a Roma, ya neme ni ido a rufe sai da ya same ni.
17 Har ma da ya zo Roma, sai ya neme ni ido a rufe, ya kuwa same ni.
Bari Ubangiji yă yi wa iyalin Onesiforus jinƙai, domin sau da dama yakan wartsakar da ni, bai kuma ji kunyar sarƙoƙina ba.
Bari Ubangiji yă sa yă sami jinƙai daga Ubangiji a wancan ranar! Ka sani sarai yadda ya taimake ni a hanyoyi dabam-dabam a Afisa.