2 Tessalonikawa 2:3 - Sabon Rai Don Kowa 20203 Kada ku bar wani yă ruɗe ku ko ta yaya, gama wannan rana ba za tă zo ba sai an yi tawayen nan an kuma bayyana mutumin tawayen nan, mutumin da aka ƙaddara ga hallaka. အခန်းကိုကြည့်ပါ။Littafi Mai Tsarki3 Kada ku yarda kowa yă yaudare ku ko ta halin ƙaƙa, domin wannan rana ba za ta zo ba, sai an yi fanɗarewar nan, sarkin tawaye kuma ya bayyana, wato, hallakakken nan. အခန်းကိုကြည့်ပါ။ |
Dabbar da ka gani, a dā ta taɓa kasancewa, a yanzu, ba ta, za tă kuma fito daga Abis zuwa ga hallakarta. Mazaunan duniya waɗanda ba a rubuta sunayensu a littafin rai tun kafin halittar duniya ba za su yi mamaki sa’ad da suka ga dabbar, domin a dā ta taɓa kasancewa, yanzu kuwa ba ta, duk da haka za tă dawo.