2 Tarihi 9:8 - Sabon Rai Don Kowa 20208 Yabo ya tabbata ga Ubangiji Allahnka, wanda ya ji daɗi a cikinka ya sa ka a kan kujerar sarautarsa a matsayin sarki don ka yi mulkin domin Ubangiji Allahnka. Saboda ƙaunar Allahnka wa Isra’ila da kuma sha’awarsa na riƙe su har abada, ya naɗa ka sarki a bisansu, don ka yi adalci da kuma gaskiya.” အခန်းကိုကြည့်ပါ။Littafi Mai Tsarki8 Yabo ya tabbata ga Ubangiji Allahnka wanda yake murna da kai, wanda ya hawar da kai gadon sarautarsa, don ka zama sarki a gaban Ubangiji Allahnka. Gama Allah yana ƙaunar Isra'ila, zai kuwa tabbatar da su har abada, shi ya sa ya naɗa ka sarkinsu, don ka aikata gaskiya da adalci.” အခန်းကိုကြည့်ပါ။ |