Ban da haka, Dawuda ya yaƙi Hadadezer ɗan Rehob, sarkin Zoba. Wannan ya faru a lokacin da Hadadezer yake kan hanyarsa zuwa Kogin Yuferites don yă sāke mai da wurin a ƙarƙashin ikonsa.
Game da sauran ayyukan mulkin Yerobowam, da dukan abin da ya yi, da yaƙe-yaƙen da ya yi, haɗe da sāke ƙwato wa Isra’ila Damaskus da Hamat waɗanda suke a hannun Yahuda, duk a rubuce suke a cikin littafin tarihin sarakunan Isra’ila.