Biblia Todo Logo
အွန်လိုင်း သမ္မာကျမ်းစာ

- ကြော်ငြာတွေ -




2 Tarihi 8:11 - Sabon Rai Don Kowa 2020

11 Solomon ya kawo ’yar Fir’auna daga Birnin Dawuda zuwa fadan da ya gina mata, gama ya ce, “Matata ba za tă zauna a fadan Dawuda sarkin Isra’ila ba, domin wuraren da akwatin alkawarin Ubangiji ya shiga masu tsarki ne.”

အခန်းကိုကြည့်ပါ။ ကော်ပီ

Littafi Mai Tsarki

11 Sulemanu kuwa ya kawo 'yar Fir'auna daga birnin Dawuda zuwa gidan da ya gina mata, gama ya ce, “Matata ba za ta zauna a gidan Dawuda, Sarkin Isra'ilawa ba, saboda duk wuraren da akwatin Ubangiji ya shiga sun tsarkaka.”

အခန်းကိုကြည့်ပါ။ ကော်ပီ




2 Tarihi 8:11
8 ပူးပေါင်းရင်းမြစ်များ  

A fadar da zai zauna kuwa, wadda aka gina a can baya, ya yi ta da irin fasali guda. Solomon ya kuma yi wata fada kamar wannan zaure domin ’yar Fir’auna, wadda ya auro.


Solomon ya haɗa kai da Fir’auna sarkin Masar, ya kuwa auri ’yarsa. Ya kawo ta cikin Birnin Dawuda kafin yă gama ginin fadarsa, da haikalin Ubangiji, da kuma katanga kewaye da Urushalima.


Bayan ’yar Fir’auna ta haura daga Birnin Dawuda zuwa fadan da Solomon ya gina mata, sai ya gina madogaran gini.


Mu kanmu mun ji wannan muryar da ta zo daga sama sa’ad da muke tare da shi a kan dutse mai tsarki.


“Ɗan mutum, ka kafa fuskarka gāba da Urushalima ka kuma yi wa’azi a kan wuri mai tsarki. Ka yi annabci gāba da ƙasar Isra’ila


a can kuma zan sadu da Isra’ilawa, in kuma tsarkake wurin da ɗaukakata.


Allah ya ce, “Kada ka zo kusa, tuɓe takalmanka, gama inda kake tsaye, wuri ne mai tsarki.”


Su ne kuma manyan ma’aikatan Sarki Solomon, manyan mutane ɗari biyu da hamsin masu lura da mutane.


ကြှနျုပျတို့နောကျလိုကျပါ:

ကြော်ငြာတွေ


ကြော်ငြာတွေ