2 Tarihi 7:20 - Sabon Rai Don Kowa 202020 zan tumɓuke Isra’ila daga ƙasata, wadda na ba su, zan kuma ƙi wannan haikalin da na tsarkake domin Sunana. Zan mai da shi abin karin magana da abin ba’a cikin dukan mutane. အခန်းကိုကြည့်ပါ။Littafi Mai Tsarki20 to, sai in tumɓuke ka daga ƙasata wadda na ba ka, wannan Haikali kuma wanda na riga na keɓe domin sunana, zan kawar da shi daga fuskata, zan kuwa maishe shi abin karin magana, abin raini ga dukan sauran al'umma. အခန်းကိုကြည့်ပါ။ |
Waɗannan mutane sun zama kamar ƙazanta a taronku na soyayya, suna ta ciye-ciye a cikinku, ba kunya ba tsoro. Su masu kiwo ne da suke ciyar da kansu kawai. Su kamar hadari ne da babu ruwa da iska take kori. Su kamar itatuwa ne, marasa ’ya’ya da rani, waɗanda aka tumɓuke, ko kamar itatuwan da aka tumɓuke suka kuma mutu ƙurmus.