2 Tarihi 6:41 - Sabon Rai Don Kowa 202041 “Yanzu ka tashi, ya Ubangiji Allah, ka zo wurin hutunka, kai da akwatin alkawarin ƙarfinka. Bari firistocinka, ya Ubangiji Allah, su sanye ceto, bari tsarkakanka su yi farin ciki cikin alherinka. အခန်းကိုကြည့်ပါ။Littafi Mai Tsarki41 Yanzu fa, ya Ubangiji ka tashi ka tafi wurin hutawarka, kai da akwatin ikonka. Ya Ubangiji Allah ka yi wa firistocinka sutura da cetonka, adalanka kuma su yi farin ciki da nagartarka. အခန်းကိုကြည့်ပါ။ |
Suka kame birane masu katanga masu ƙarfi, da ƙasa masu ba da amfani; suka mallaki gidaje cike da kowane irin abu mai kyau, da rijiyoyin da aka riga aka haƙa, da gonakin inabi, da gonakin itatuwan zaitun da kuma itatuwan ba da ’ya’ya a yalwace a ciki. Suka ci suka ƙoshi, suka kuma yi ƙiba; suka ji daɗi cikin alherinka mai girma.