Biblia Todo Logo
အွန်လိုင်း သမ္မာကျမ်းစာ

- ကြော်ငြာတွေ -




2 Tarihi 6:34 - Sabon Rai Don Kowa 2020

34 “Sa’ad da mutanenka suka je yaƙi da abokan gābansu, ko’ina ka kai su, kuma sa’ad da suka yi addu’a gare ka suna duban wannan birnin da ka zaɓa da haikalin nan da na gina domin Sunanka,

အခန်းကိုကြည့်ပါ။ ကော်ပီ

Littafi Mai Tsarki

34 “Sa'ad da jama'arka za su fita don yin yaƙi da magabtansu, duk dai ko ta ina ne za ka aike su, in sun yi addu'a gare ka, suna fuskantar wannan birni wanda kai ka zaɓa, da Haikalin nan da na gina saboda sunanka,

အခန်းကိုကြည့်ပါ။ ကော်ပီ




2 Tarihi 6:34
19 ပူးပေါင်းရင်းမြစ်များ  

To, da Daniyel ya ji labarin cewa an fitar da doka, sai ya tafi gidansa a ɗakinsa na sama inda tagogin ɗakin suke duban wajen Urushalima. Sau uku yakan durƙusa yă yi addu’a yana yin godiya ga Allahnsa, kamar yadda ya saba yi.


Wace amsa ce za a bayar wa jakadun wannan al’umma? “Ubangiji ya kafa Sihiyona, kuma a cikinta mutanensa masu shan azaba za su sami mafaka.”


Mutanen Yahuda suka taru gaba ɗaya don su nemi taimako daga wurin Ubangiji, tabbatacce suka fito daga kowane garin Yahuda don su neme shi.


Sa’ad da shugabannin kekunan yaƙi suka ga Yehoshafat, sai suka yi tsammani, “Wannan ne sarkin Isra’ila.” Saboda haka suka juya don su yaƙe shi, amma Yehoshafat ya yi ihu, Ubangiji kuma ya taimake shi. Allah ya janye su daga gare shi,


Amma yanzu na zaɓi Urushalima domin Sunana yă kasance a can, na kuma zaɓi Dawuda yă yi mulkin mutanena Isra’ila.’


ga shi na gina haikali mai daraja dominka, inda za ka zauna har abada.”


Shi kuma ya aika, ya umarce ka cewa, ‘Tafi ka hallaka Amalekawa mugayen mutanen nan duka, ka yaƙe su sai ka share su ƙaf.’


Yanzu ka tafi ka yaƙi Amalekawa, ka hallaka kome da yake nasu, kada ka bar su da rai, ka kashe maza, da mata, da yara, da jarirai, da dabbobi, da tumaki, da raƙuma, da kuma jakuna.’ ”


sai ka ji daga sama, mazauninka, ka kuma yi duk abin da baƙon ya nemi ka yi, saboda dukan mutanen duniya su san sunanka su kuma ji tsoronka, kamar yadda mutanenka Isra’ila suke yi, su kuma san cewa wannan gidan da na gina na Sunanka ne.


sai ka ji addu’arsu da kuma roƙonsu daga sama, ka kuma biya musu bukatarsu.


ကြှနျုပျတို့နောကျလိုကျပါ:

ကြော်ငြာတွေ


ကြော်ငြာတွေ