Biblia Todo Logo
အွန်လိုင်း သမ္မာကျမ်းစာ

- ကြော်ငြာတွေ -




2 Tarihi 6:16 - Sabon Rai Don Kowa 2020

16 “Yanzu fa Ubangiji, Allah na Isra’ila, ka kiyaye wa bawanka Dawuda mahaifina alkawuran da ka yi masa sa’ad da ka ce, ‘Ba za ka kāsa kasance da mutumin da zai zauna a gabana a kan kujerar sarautar Isra’ila ba, in kawai ’ya’yanka maza za su kula cikin dukan abin da suke yi su yi tafiya a gabana bisa ga dokata, kamar yadda ka yi.’

အခန်းကိုကြည့်ပါ။ ကော်ပီ

Littafi Mai Tsarki

16 Yanzu fa, ya Ubangiji, Allah na Isra'ila, ka cika alkawarin da ka yi wa bawanka tsohona cewa, ‘Daɗai, ba za a rasa wanda zai hau gadon sarautar Isra'ila ba, in dai 'ya'yanka maza za su lura da al'amuransu, don su yi tafiya bisa ga shari'ata, yadda kai ka yi tafiya a gabana.’

အခန်းကိုကြည့်ပါ။ ကော်ပီ




2 Tarihi 6:16
16 ပူးပေါင်းရင်းမြစ်များ  

Ubangiji kuwa zai kiyaye alkawarinsa gare ni da ya ce, ‘In zuriyarka suka lura da yadda suke rayuwa, in kuma suka yi tafiya da aminci a gabana da dukan zuciyarsu, da kuma dukan ransu, ba za ka kāsa samun mutum a kujerar sarautar Isra’ila ba.’


in ’ya’yanka maza za su kiyaye alkawari da farillan da na koya musu, to ’ya’yansu maza za su zauna a kan kursiyinka har abada abadin.”


zan kafa kujerar sarautarka, yadda na alkawarta wa Dawuda mahaifinka sa’ad da na ce, ‘Ba za ka taɓa rasa wani mutumin da zai yi mulki a bisa Isra’ila ba.’


“Ga abin da Ubangiji Mai Iko Duka yana cewa har yanzu zan ji roƙon gidan Isra’ila in kuma yi musu wannan. Zan sa mutanensu su yi yawa kamar tumaki,


Albarka ta tabbata ga waɗanda rayuwarsu ba ta da abin zargi, waɗanda suke tafiya bisa ga dokar Ubangiji.


gama ƙaunarka kullum tana a gabana, kuma ina cin gaba da tafiya a cikin gaskiyarka.


“Game da wannan haikalin da kake ginawa, in ka bi ƙa’idodina, ka cika farillaina, ka kiyaye dukan umarnaina, ka kuma yi biyayya da su, zan cika alkawarin da na yi wa mahaifinka Dawuda ta wurinka.


Yanzu kuwa, ya Ubangiji, Allah na Isra’ila, bari maganarka da ka yi alkawarta wa bawanka Dawuda yă cika.


Yaya matashi zai kiyaye hanyarsa da tsabta? Sai ta yin rayuwa bisa ga maganarka.


Ubangiji ya rantse wa Dawuda tabbataccen rantsuwa cewa ba zai janye ba cewa, “Ɗaya daga cikin zuriyarka zan sa a kan kursiyinka,


“Game da kai kuwa, in ka yi tafiya a gabana kamar yadda Dawuda mahaifinka ya yi, ka kuma yi dukan abin da na umarta, ka kiyaye ƙa’idodina da dokokina,


Ba ku san cewa Ubangiji, Allah na Isra’ila ya ba da sarautar Isra’ila ga Dawuda da zuriyarsa har abada ta wurin alkawarin gishiri ba?


Duk da haka, domin alkawarin da Ubangiji ya yi wa Dawuda, Ubangiji bai so yă hallaka gidan Dawuda ba. Ubangiji ya riga ya yi alkawari zai ci gaba da riƙe fitila domin Dawuda da zuriyarsa har abada.


dukan taron suka yi alkawari da sarki a haikalin Allah. Yehohiyada ya ce musu, “Ɗan sarki zai yi mulki yadda Ubangiji ya yi alkawari game da zuriyar Dawuda.


ကြှနျုပျတို့နောကျလိုကျပါ:

ကြော်ငြာတွေ


ကြော်ငြာတွေ