Biblia Todo Logo
အွန်လိုင်း သမ္မာကျမ်းစာ

- ကြော်ငြာတွေ -




2 Tarihi 6:13 - Sabon Rai Don Kowa 2020

13 Dā ma ya riga ya gina dakalin tagulla, mai tsawo kamu biyar, fāɗi kamu biyar da kuma tsayi kamu uku, ya kuma sa shi a tsakiyar filin waje. Ya tsaya a kan dakalin ya kuma durƙusa a gaban dukan taron Isra’ila ya buɗe hannuwansa sama.

အခန်းကိုကြည့်ပါ။ ကော်ပီ

Littafi Mai Tsarki

13 Sulemanu ya riga ya yi dakali na tagulla, tsawonsa kamu biyar, fāɗinsa kamu biyar, tsayinsa kamu uku, ya ajiye shi a tsakiyar filin, ya tsaya a kai. Ya durƙusa a gwiwoyinsa, a idon dukan taron jama'ar Isra'ila, ya ɗaga hannuwansa sama,

အခန်းကိုကြည့်ပါ။ ကော်ပီ




2 Tarihi 6:13
14 ပူးပေါင်းရင်းမြစ်များ  

Da Solomon ya gama dukan waɗannan addu’o’i da roƙe-roƙe ga Ubangiji, sai ya tashi daga gaban bagaden Ubangiji, inda ya durƙusa da hannuwansa a buɗe waje sama.


Ezra malamin Doka ya tsaya a kan dakalin itacen da aka yi saboda wannan hidima. Kusa da shi a damansa, Mattitiya, Shema, Anahiya, Uriya, Hilkiya da Ma’asehiya suka tsaya; a hagunsa kuma Fedahiya, Mishayel, Malkiya, Hashum, Hashbaddana, Zakariya da Meshullam suka tsaya.


Ku zo, bari mu rusuna mu yi sujada, bari mu durƙusa a gaban Ubangiji Mahaliccinmu;


Sa’an nan a lokacin miƙa hadaya na yamma, na tashi da ɓacin raina, da yagaggun kayana, na durƙusa na miƙa hannuwana sama ga Ubangiji Allahna


Amma da lokacin tashinmu ya yi, sai muka tashi muka ci gaba da tafiyarmu. Dukan almajirai da matansu da ’ya’yansu suka raka mu har bayan birni, a can kuwa a bakin teku muka durƙusa muka yi addu’a.


Da ya faɗi haka, ya durƙusa tare da dukansu ya yi addu’a.


Sai ya janye daga wurinsu, misalin nisan jifa, ya durƙusa a ƙasa ya yi addu’a,


To, da Daniyel ya ji labarin cewa an fitar da doka, sai ya tafi gidansa a ɗakinsa na sama inda tagogin ɗakin suke duban wajen Urushalima. Sau uku yakan durƙusa yă yi addu’a yana yin godiya ga Allahnsa, kamar yadda ya saba yi.


Ya yi fili na firistoci da kuma babban fili da ƙofofi domin filin, ya shafe ƙofofin da tagulla.


An kewaye babban filin da katanga da jerin uku-uku na duwatsun da aka gyara, da kuma jeri guda na gyararren al’ul, kamar yadda aka yi na filin cikin haikalin Ubangiji da shirayinsa.


Ya kuma gina filin ciki da sassaƙaƙƙun duwatsu, jeri uku, da jeri ɗaya na katakan itacen al’ul.


Sa’an nan Solomon ya tsaya a gaban bagaden Ubangiji a gaban dukan taron Isra’ila ya ɗaga hannuwansa sama.


Musa ya amsa, “To, da kyau, da zarar na fita daga birnin, zan yi addu’a ga Ubangiji, tsawar za tă tsaya, ƙanƙarar kuma za tă daina, don ku sani cewa duniya ta Ubangiji ce.


Da na ji waɗannan abubuwa, sai na zauna na yi kuka. Na yi kwanaki ina makoki da azumi, na kuma yi addu’a a gaban Allah na sama.


ကြှနျုပျတို့နောကျလိုကျပါ:

ကြော်ငြာတွေ


ကြော်ငြာတွေ