2 Tarihi 5:2 - Sabon Rai Don Kowa 20202 Sa’an nan Solomon ya tattara zuwa Urushalima dattawan Isra’ila, dukan kawunan kabilu da manyan iyalan Isra’ilawa, don su haura da akwatin alkawarin Ubangiji daga Sihiyona, Birnin Dawuda. အခန်းကိုကြည့်ပါ။Littafi Mai Tsarki2 Sulemanu kuwa ya tattara dattawan Isra'ila, da shugabannin kabilai, da shugabannin gidajen kakannin jama'ar Isra'ila, a Urushalima, domin a yi bikin fito da akwatin alkawari na Ubangiji da yake a alfarwa a birnin Dawuda, wato Sihiyona. အခန်းကိုကြည့်ပါ။ |
Dawuda ya sa aka kira dukan shugabannin Isra’ila su taru a Urushalima, shugabannin kabilu, manyan hafsoshin ɓangarorin hidimar sarki, manyan hafsoshin dubu-dubu da manyan hafsoshin ɗari-ɗari, da kuma shugabanni masu lura da dukan mallaka da dabbobin da suke na sarki da kuma ’ya’yansa maza, tare da fadawa, jarumawa da kuma dukan mayaƙa masu kwarjini.