2 Tarihi 5:12 - Sabon Rai Don Kowa 202012 Dukan Lawiyawa waɗanda suke mawaƙa, Asaf, Heman, Yedutun da ’ya’yansu maza da dangoginsu, suka tsaya a gefen gabas na bagaden, saye da lilin mai kyau suna kuma kaɗa ganguna, garayu da molaye. Tare da su akwai firistoci 120 masu busan ƙahoni. အခန်းကိုကြည့်ပါ။Littafi Mai Tsarki12 Dukan Lawiyawa mawaƙa, wato su Asaf, da Heman, da Yedutun tare da 'ya'yansu maza da 'yan'uwansu, aka sa su su tsaya a gabashin bagade, suna sāye da lilin mai kyau, suna ta kaɗa kuge, da molaye da garayu, ga kuma firistoci ɗari da ashirin masu busa ƙaho tare da su. အခန်းကိုကြည့်ပါ။ |
Firistoci suka ɗauki matsayinsu, haka kuma Lawiyawa suka tsaya a matsayinsu riƙe da kayansu na bushe-bushe da na kaɗe-kaɗe na Ubangiji, waɗanda Sarki Dawuda ya yi domin yabon Ubangiji. An yi amfani da su sa’ad da ake godiya, ana kuma cewa, “Ƙaunarsa dawwammamiya ce har abada.” Kurkusa da Lawiyawa, firistoci suka busa ƙahoninsu, dukan Isra’ila kuwa suna a tsaye.