15 ya yi kwanon da ya kira Teku, da bijimai goma sha biyu a ƙarƙashinsa;
dakalai da darunansu;
tukwane, manyan cokula, cokula masu yatsu don nama da dukan kayayyakin da suka shafi wannan. Dukan kayayyakin da Huram-Abi ya yi domin Sarki Solomon saboda haikalin Ubangiji an yi su da gogaggen tagulla ne.