2 Tarihi 34:3 - Sabon Rai Don Kowa 20203 A shekara ta takwas ta mulkinsa, yayinda yake matashi, sai ya fara neman Allah na kakansa Dawuda. A shekara ta goma sha biyunsa ya fara tsabtacce Yahuda da Urushalima daga masujadan kan tudu, ginshiƙan Ashera, sassaƙaƙƙun gumaka da kuma siffofin da aka yi zubi. အခန်းကိုကြည့်ပါ။Littafi Mai Tsarki3 A shekara ta takwas ta mulkinsa, a lokacin yana yaro, sai ya fara neman Allah na kakansa Dawuda. A shekara ta goma, sha biyu, sai ya fara tsarkake Yahuza da Urushalima daga masujadai, da Ashtarot, da sassaƙaƙƙun siffofi, da siffofi na zubi. အခန်းကိုကြည့်ပါ။ |
Sai Yosiya ya umarci Hilkiya babban firist, tare da firistocin da suke taimakonsa, da masu tsaron ƙofa su kawar da dukan abubuwan da aka yi domin Ba’al, da domin Ashera, da kuma domin dukan rundunar taurari, daga haikalin Ubangiji. Ya ƙone su a bayan Urushalima a filayen Kwarin Kidron, ya kwashe tokan zuwa Betel.