4 Shirin ya yi kyau ga sarki da kuma dukan taron.
4 A ganin sarki da na jama'a duka, shirin ya yi daidai.
Dukan taron jama’a suka yarda su yi haka, domin ya yi daidai ga dukan mutane.
Ba su iya yinsa a daidai lokacinsa ba domin babu isashen firistocin da suka tsarkake kansu, mutane kuma ba su taru a Urushalima ba.
Suka yanke shawara su yi shelar a ko’ina a Isra’ila, daga Beyersheba zuwa Dan, suna kiran mutane su zo Urushalima, suka kuma yi Bikin Ƙetarewa ga Ubangiji Allah na Isra’ila. Ba a yi bikin da mutane masu yawa bisa ga abin da aka rubuta ba.