2 Tarihi 3:6 - Sabon Rai Don Kowa 20206 Ya yi wa haikalin ado da duwatsu masu daraja. Zinariyar da ya yi amfani da su kuwa zinariya Farwayim ne. အခန်းကိုကြည့်ပါ။Littafi Mai Tsarki6 Banda wannan kuma ya ƙawata Haikalin da duwatsu masu daraja da zinariya irin ta Farwayim. အခန်းကိုကြည့်ပါ။ |
Na riga na tara dukan kayayyakin da na tanada saboda haikalin Allahna, zinariya saboda dukan ayyukan zinariya, azurfa saboda ayyukan azurfa, tagulla saboda ayyukan tagulla, ƙarfe saboda ayyukan ƙarfe da kuma katako saboda ayyukan katako, da onis don ado, turkuwoyis, duwatsu masu launi dabam-dabam, da kuma dukan duwatsu masu kyau da mabul, dukan waɗannan suna nan jingim.