2 Tarihi 23:3 - Sabon Rai Don Kowa 20203 dukan taron suka yi alkawari da sarki a haikalin Allah. Yehohiyada ya ce musu, “Ɗan sarki zai yi mulki yadda Ubangiji ya yi alkawari game da zuriyar Dawuda. အခန်းကိုကြည့်ပါ။Littafi Mai Tsarki3 Sai dukan taron suka yi wa sarki alkawari, a Haikalin Allah. Yehoyada ya ce musu, “Wannan shi ne ɗan sarki, sai ya ci sarauta kamar yadda Ubangiji ya faɗa a kan 'ya'yan Dawuda, maza. အခန်းကိုကြည့်ပါ။ |
“Yanzu fa Ubangiji, Allah na Isra’ila, ka kiyaye wa bawanka Dawuda mahaifina alkawuran da ka yi masa sa’ad da ka ce, ‘Ba za ka kāsa kasance da mutumin da zai zauna a gabana a kan kujerar sarautar Isra’ila ba, in kawai ’ya’yanka maza za su kula cikin dukan abin da suke yi su yi tafiya a gabana bisa ga dokata, kamar yadda ka yi.’