2 Tarihi 19:9 - Sabon Rai Don Kowa 20209 Ya ba su waɗannan umarnai, “Ku yi aikinku da aminci da tsoron Ubangiji da dukan zuciyarku. အခန်းကိုကြည့်ပါ။Littafi Mai Tsarki9 Sai ya umarce su ya ce, “Haka za ku yi saboda tsoron Ubangiji, ku yi aminci, ku yi da zuciya ɗaya kuma. အခန်းကိုကြည့်ပါ။ |
Cikin kowane batun da ya zo gabanku daga ’yan’uwanku waɗanda suke zama a birane, ko batun na kisa ne ko kuwa waɗansu batuttuwan da suka shafi doka, umarnai, ƙa’idodi ko farillai, dole ku ja musu kunne kada su yi wa Ubangiji zunubi; in ba haka ba fushinsa zai sauko a kanku da ’yan’uwanku. Ku yi wannan, ta haka ba za ku kuwa yi zunubi ba.