2 Tarihi 15:8 - Sabon Rai Don Kowa 20208 Sa’ad da Asa ya ji waɗannan kalmomin da annabcin Azariya ɗan Oded annabi ya faɗa, sai ya sami ƙarfi hali. Ya kawar da gumaka masu banƙyama daga dukan ƙasar Yahuda da Benyamin da kuma daga garuruwan da ya ci da yaƙi a ƙasar tudu ta Efraim. Ya gyaggyara bagaden Ubangiji da yake a gaban shirayin haikalin Ubangiji. အခန်းကိုကြည့်ပါ။Littafi Mai Tsarki8 Da Asa ya ji irin kalmomin da annabi Azariya ɗan Oded ya hurta, sai ya yi ƙarfin zuciya, ya kawar da gumakan nan masu banƙyama daga dukan ƙasar Yahuza da ta Biliyaminu, daga kuma biranen da ya ci a ƙasar tuddai na Ifraimu. Sa'an nan ya gyara bagaden Ubangiji wanda yake a ƙofar shirayin Haikalin Ubangiji. အခန်းကိုကြည့်ပါ။ |
“Amariya, babban firist, shi ne zai shugabance ku a kan dukan al’amuran da suke na wajen Ubangiji, Zebadiya ɗan Ishmayel kuwa, shugabanku a kan dukan al’amuran da suka shafi sarki, Lawiyawa kuma za su zama a matsayin manya a gabanku. Ku yi abubuwa da ƙarfin hali, bari kuma Ubangiji yă kasance tare da masu yin gaskiya.”