Sai Ruhun Allah ya sauko a kan Zakariya ɗan Yehohiyada firist. Ya tsaya a gaban mutane ya ce, “Ga abin da Allah ya ce, ‘Me ya sa ba ku yi biyayya da umarnan Ubangiji ba? Ba za ku yi nasara ba. Domin kun yashe Ubangiji, shi ma ya yashe ku.’ ”
Sa’an nan Ruhun Ubangiji ya sauko a kan Yahaziyel ɗan Zakariya, ɗan Benahiya, ɗan Yehiyel, ɗan Mattaniya, wani Balawe kuma zuriyar Asaf, yayinda yake tsaye a cikin taron.
Ruhun Ubangiji ya sauko masa, domin yă zama mahukuncin Isra’ila yă kuma je yaƙi. Ubangiji ya bayar da Kushan-Rishatayim sarkin Aram a hannun Otniyel, ya kuwa sha ƙarfinsa.
To, fa, akwai dattawa biyu da suka kasance a sansani, wato, Eldad da Medad. Su ma an lasafta su cikin dattawan, amma ba su fita zuwa Tentin Sujada ba. Duk da haka Ruhun ya sauka a kansu, suka kuma yi annabci a cikin sansanin.