2 Tarihi 14:7 - Sabon Rai Don Kowa 20207 Ya ce wa Yahuda, “Bari mu gina waɗannan garuruwa mu sa katanga kewaye da su, da hasumiyoyi, ƙofofi da ƙyamare. Ƙasar har yanzu tamu ce domin mun nemi Ubangiji Allahnmu, mun neme shi ya kuwa ba mu hutu a kowane gefe.” Saboda haka suka gina suka kuma yi nasara. အခန်းကိုကြည့်ပါ။Littafi Mai Tsarki7 Sai ya ce wa mutanen Yahuza, “Bari mu giggina waɗannan birane, mu kewaye su da garu, da hasumiya, da ƙofofi masu ƙyamare. Ƙasar tamu ce har yanzu, saboda mun nemi Ubangiji Allahnmu. Mun neme shi, ya kuwa ba mu salama a kowace fuska.” Suka yi ta gini, suka kuwa arzuta. အခန်းကိုကြည့်ပါ။ |
Amaziya ya tattara mutanen Yahuda ya kuma ba su aiki bisa ga iyalansu, ya ba da aiki ga shugabannin dubu-dubu da shugabannin ɗari-ɗari, a dukan Yahuda da Benyamin. Ya kuma tattara waɗanda suke ’yan shekara ashirin da haihuwa ko fiye ya sami mutane dubu ɗari uku da suke a shirye don aikin soja, da suka isa riƙe māshi da garkuwa.