Sarki Rehobowam ya kafa kansa daram a Urushalima, ya kuma ci gaba a matsayin sarki. Yana da shekara arba’in da ɗaya sa’ad da ya zama sarki, ya kuma yi mulki shekara goma sha bakwai a Urushalima, birnin da Ubangiji ya zaɓa daga dukan kabilan Isra’ila wanda zai sa Sunansa. Sunan mahaifiyarsa Na’ama ce, ita mutuniyar Ammon ce.