Biblia Todo Logo
အွန်လိုင်း သမ္မာကျမ်းစာ

- ကြော်ငြာတွေ -




2 Tarihi 11:21 - Sabon Rai Don Kowa 2020

21 Rehobowam ya ƙaunaci Ma’aka ’yar Absalom fiye da sauran matansa da ƙwarƙwaransa. Duka-duka dai ya auri mata goma sha takwas da ƙwarƙwarai sittin, yana da ’ya’ya maza ashirin da takwas da ’ya’ya mata sittin.

အခန်းကိုကြည့်ပါ။ ကော်ပီ

Littafi Mai Tsarki

21 Rehobowam ya fi ƙaunar Ma'aka, 'yar Absalom, fiye da dukan matansa, da ƙwaraƙwaransa. Yana kuwa da matan aure goma sha takwas, da ƙwaraƙwarai sittin. 'Ya'yan da ya haifa maza ashirin da takwas ne, 'ya'ya mata kuwa sittin.

အခန်းကိုကြည့်ပါ။ ကော်ပီ




2 Tarihi 11:21
11 ပူးပေါင်းရင်းမြစ်များ  

Sarkin ba zai auri mata masu yawa ba, in ba haka ba zuciyarsa za tă karkata. Ba zai tara azurfa da zinariya da yawa ba.


Ya auri mata ɗari bakwai, haifaffun gidan sarauta, da kuma ƙwarƙwarai ɗari uku. Matan nan nasa suka karkatar da shi.


Bayan ya bar Hebron, Dawuda ya ƙara ɗauko wa kansa waɗansu ƙwarƙwarai da mata a Urushalima. Aka haifa masa ’ya’ya maza da mata.


Yana da ’ya’ya saba’in maza da ya haifa, gama yana da mata da yawa.


Ya yi hikima, ya watsar da waɗansu ’ya’yansa a dukan yankunan Yahuda da Benyamin, da kuma a dukan birane masu katanga. Ya ba su tanadi mai yawa ya kuma aurar musu mata masu yawa.


Ban da haka ma, ƙwarƙwararsa, mai suna Reyuma, ta haifa masa ’ya’ya maza, Teba, Gaham, Tahash da kuma Ma’aka.


ya kuma yi mulki a Urushalima shekara uku. Sunan mahaifiyarsa Ma’aka ne, ’yar Abisalom.


to, a ranar da zai yi faɗa wane ne a cikin ’ya’yansa zai riƙe gādon da zai bar musu, kada yă sa ɗan matar da yake ƙauna yă zama kamar shi ne ɗan fari, a maimakon ɗan matar da ba ya ƙauna, wanda shi ne ɗan farin.


ကြှနျုပျတို့နောကျလိုကျပါ:

ကြော်ငြာတွေ


ကြော်ငြာတွေ