Biblia Todo Logo
အွန်လိုင်း သမ္မာကျမ်းစာ

- ကြော်ငြာတွေ -




2 Sarakuna 9:20 - Sabon Rai Don Kowa 2020

20 Mai tsaro ya sāke cewa, “Ya kai wurinsu, amma shi ma ba ya dawowa. Ina ganin sukuwar kamar irin ta Yehu, jikan Nimshi, gama yakan yi sukuwa kamar mahaukaci.”

အခန်းကိုကြည့်ပါ။ ကော်ပီ

Littafi Mai Tsarki

20 Mai tsaro ya sāke cewa, “Ya kai wurinsu, amma bai komo ba. Ina ganin sukuwar kamar irin ta Yehu, jikan Nimshi, gama yakan yi sukuwa da hauka.”

အခန်းကိုကြည့်ပါ။ ကော်ပီ




2 Sarakuna 9:20
10 ပူးပေါင်းရင်းမြစ်များ  

Sai mai tsaron ya ce, “A ganina gudu na farin, ya yi kama da gudun Ahimawaz, ɗan Zadok.” Sarki ya ce, “Shi mutumin kirki ne, yana zuwa da saƙo mai kyau.”


Cikin hasala ka ratsa duniya cikin fushi kuma ka tattake ƙasashe.


Zan tā da Babiloniyawa, waɗannan marasa hankali da kuma marasa tausayi; masu gajeren haƙuri, waɗanda suke ratsa ko’ina a duniya don su ƙwace wuraren zaman da ba nasu ba.


Amma labari daga gabas da arewa za su firgita shi, shi kuwa zai ci gaba da yin yaƙi da zafi, yă karkashe mutane da yawa, yă shafe su.


“Duba, ni ne wanda na halicci maƙeri wanda yake zuga garwashi ya zama harshen wuta ya kuma ƙera makamin da ya dace da aikinsa. Ni ne kuma na halicci mai hallakarwa ya yi ɓarna;


Duk abin da hannunka yake yi, ka yi shi da dukan ƙarfinka, gama a cikin kabari in da za ka, babu aiki ko shirye-shirye, ko sani, ko hikima.


Yehu ya ce, “Zo tare da ni ka ga himmata saboda Ubangiji.” Sa’an nan ya sa suka tafi tare cikin keken yaƙinsa.


Yehu zai kashe duk wani wanda ya tsere wa takobin Hazayel, Elisha kuwa zai kashe duk wani wanda ya tsere wa takobin Yehu.


Da ka isa can, ka nemi Yehu ɗan Yehoshafat, ɗan Nimshi. Ka je wurinsa, ka ja shi gefe daga abokansa, ka shiga da shi ɗaki na ciki.


Saboda haka sarki ya sāke aika mahayin doki na biyu. Sa’ad da ya isa wurinsu sai ya ce, “Ga abin da sarki ya ce, ‘Lafiya?’ ” Yehu ya ce, “Ina ruwanka da zancen lafiya? Ka shiga layi.”


ကြှနျုပျတို့နောကျလိုကျပါ:

ကြော်ငြာတွေ


ကြော်ငြာတွေ