2 Sarakuna 9:11 - Sabon Rai Don Kowa 202011 Da Yehu ya koma wurin sauran hafsoshin sai ɗaya daga cikinsu ya tambaye shi, “Lafiya? Me ya kawo wannan mahaukaci a wurinka?” Sai Yehu ya ce, “Ka san mahaukacin nan da irin maganganunsa.” အခန်းကိုကြည့်ပါ။Littafi Mai Tsarki11 Da Yehu ya fita zuwa wurin sauran shugabannin, sai suka tambaye shi, “Lafiya kuwa, me ya sa mahaukacin nan ya zo wurinka?” Sai ya ce musu, “Ai, kun san mutumin da irin maganarsa.” အခန်းကိုကြည့်ပါ။ |
Wata ƙungiyar Afikuriya da kuma masu bin ussan ilimin Sitoyik suka fara gardama da shi. Waɗansunsu suka ce, “Mene ne mai surutun nan yake ƙoƙarin faɗi?” Waɗansu suka ce, “Kamar yana wa’azin baƙin alloli ne.” Sun faɗa haka ne domin Bulus yana wa’azin labari mai daɗi game da Yesu da kuma tashin matattu.