2 Sarakuna 8:6 - Sabon Rai Don Kowa 20206 Sarki ya tambayi macen game da al’amarin, ita kuwa ta faɗa masa. Sa’an nan ya sa wani hafsa yă dubi damuwarta ya kuma ce masa, “Ka mayar mata kome da yake nata, haɗe da dukan kuɗin da aka samo daga filin, daga ranar da ta bar ƙasar har yă zuwa yanzu.” အခန်းကိုကြည့်ပါ။Littafi Mai Tsarki6 Da sarki ya tambayi matar sai ta faɗa masa dukan labarin. Sarki kuwa ya sa wani bafade ya mayar mata da dukan abin da yake nata da dukan amfanin gonakin, tun daga ran da ta bar ƙasar har ranar da ta komo. အခန်းကိုကြည့်ပါ။ |
Dawuda ya sa aka kira dukan shugabannin Isra’ila su taru a Urushalima, shugabannin kabilu, manyan hafsoshin ɓangarorin hidimar sarki, manyan hafsoshin dubu-dubu da manyan hafsoshin ɗari-ɗari, da kuma shugabanni masu lura da dukan mallaka da dabbobin da suke na sarki da kuma ’ya’yansa maza, tare da fadawa, jarumawa da kuma dukan mayaƙa masu kwarjini.