2 Sarakuna 8:5 - Sabon Rai Don Kowa 20205 A sa’ad da Gehazi yana cikin ba shi labarin yadda Elisha ya tā da matacce ke nan, sai ga macen da aka tā da ɗanta daga matattu ta shigo don tă roƙi sarki yă mayar mata da gidanta da filinta. Gehazi ya ce, “Ranka yă daɗe, ai, ga macen, ga kuma ɗan da Elisha ya tā da daga matattu.” အခန်းကိုကြည့်ပါ။Littafi Mai Tsarki5 A sa'ad da yake faɗa wa sarki yadda Elisha ya ta da matacce, sai ga matar da ya ta da ɗanta daga matattu, ta zo ta roƙi sarki ya mayar mata da gidanta da gonarta. Sai Gehazi ya ce, “Ran sarki ya daɗe, ai, ga matar, ga kuma yaronta wanda Elisha ya tashe shi daga matattu.” အခန်းကိုကြည့်ပါ။ |
Matarsa Zeresh, da dukan abokansa suka ce masa, “Ka sa a gina wurin rataye mai laifi, mai tsawo, ƙafa saba’in da biyar, da safe kuwa ka ce wa sarki a rataye Mordekai a kansa. Sa’an nan ka tafi cin abincin dare tare da sarki da murna.” Wannan shawarar ta faranta wa Haman rai, ya kuma sa aka gina wurin rataye mai laifi.