2 Sarakuna 8:12 - Sabon Rai Don Kowa 202012 Hazayel ya ce masa, “Me ya sa ranka yă daɗe yake kuka?” Elisha ya amsa, “Domin na san illar da za ka yi wa Isra’ilawa. Za ka ƙona biranensu masu katanga, ka karkashe majiya ƙarfinsu da takobi, ka fyaffyaɗe ƙananan yaransu da ƙasa, ka tsattsage matansu masu ciki.” အခန်းကိုကြည့်ပါ။Littafi Mai Tsarki12 Hazayel ya ce, “Me ya sa shugabana yake kuka?” Elisha ya amsa ya ce, “Domin na san irin muguntar da za ka yi wa jama'ar Isra'ila. Za ka ƙone kagaransu da wuta, ka karkashe samarinsu da takobi, za ka kuma fyaffyaɗe ƙananansu a ƙasa, ka tsattsage matansu masu ciki.” အခန်းကိုကြည့်ပါ။ |
Amma Yowash sarkin Yahuda ya kwashe tsarkakan kayan da kakanninsa, Yehoshafat, Yehoram da Ahaziya, sarakunan Yahuda suka keɓe, da kyautai da shi kansa ya keɓe, da kuma dukan azurfan da aka samu a ɗakunan ajiya haikalin Ubangiji da na fada, ya aika da su wa Hazayel sarkin Aram, shi kuma ya janye daga Urushalima.