2 Sarakuna 7:17 - Sabon Rai Don Kowa 202017 Sai ya kasance cewa Sarki ya sa dogari wanda ya raka shi wajen Elisha ya tsare ƙofar birnin. Sai mutane suka tattake shi a ƙofar har ya mutu, kamar yadda annabi Elisha ya faɗa sa’ad da sarki ya tafi wurinsa. အခန်းကိုကြည့်ပါ။Littafi Mai Tsarki17 Sarki kuwa ya sa dogari wanda ya raka shi wajen Elisha ya tsare ƙofar birnin. Sai mutane suka tattake shi a ƙofar har ya mutu, kamar yadda annabi Elisha ya faɗa sa'ad da sarki ya tafi wurinsa. အခန်းကိုကြည့်ပါ။ |
To, Elisha yana zaune a cikin gidansa, dattawa kuwa suna zaune tare da shi. Sai sarki ya aiki ɗan aika yă ci gaba, amma kafin ɗan aikan yă isa, Elisha ya ce wa dattawan, “Kun gani ko? Wannan mai kisa ya aiko a cire mini kai! To, idan ɗan aikan ya iso, sai ku rufe ƙofar da ƙarfi, ku bar shi a waje. Ba da jimawa ba, maigidansa zai bi bayansa?”