Saboda haka suka je suka kira masu tsaron ƙofar birni, suka ce musu, “Mun je sansanin Arameyawa, ga shi kuwa ba mu iske kowa a can ba, babu ko motsin wani, sai dai dawakai da jakuna a daure, tentunan kuwa suna nan yadda suke.”
Sai sarki ya tashi da daren nan ya ce wa hafsoshinsa, “Na san abin da Arameyawan suke shiri! Sun san game da yunwar da muke ciki a nan, domin haka sun bar sansaninsu suka shiga jeji suka ɓuya, suna nufin sa’ad da muka fita daga birni, sai su kama mu da rai, sa’an nan su shiga birnin.”