2 Sarakuna 6:32 - Sabon Rai Don Kowa 202032 To, Elisha yana zaune a cikin gidansa, dattawa kuwa suna zaune tare da shi. Sai sarki ya aiki ɗan aika yă ci gaba, amma kafin ɗan aikan yă isa, Elisha ya ce wa dattawan, “Kun gani ko? Wannan mai kisa ya aiko a cire mini kai! To, idan ɗan aikan ya iso, sai ku rufe ƙofar da ƙarfi, ku bar shi a waje. Ba da jimawa ba, maigidansa zai bi bayansa?” အခန်းကိုကြည့်ပါ။Littafi Mai Tsarki32 Elisha kuwa yana zaune a gidansa, dattawa kuma suna zaune tare da shi. Sai sarki ya aiki mutum, amma kafin mutumin ya isa, sai Elisha ya ce wa dattawan, “Kun ga yadda mai kisankan nan ya aiko don a fille mini kai? Idan mutumin ya zo, sai ku rufe ƙofar, ku riƙe ta da ƙarfi. Ba da jimawa ba sarki zai bi bayansa.” အခန်းကိုကြည့်ပါ။ |