Biblia Todo Logo
အွန်လိုင်း သမ္မာကျမ်းစာ

- ကြော်ငြာတွေ -




2 Sarakuna 4:39 - Sabon Rai Don Kowa 2020

39 Ɗaya daga cikin mutanen ya shiga gona don neman ganyaye, ya kuwa sami kabewar jeji. Ya tsinko ’ya’yanta cike da shafin rigarsa. Da ya dawo, sai ya yayyanka su ya zuba a cikin tukunyar faten, ko da yake ba wanda ya san ko mene ne.

အခန်းကိုကြည့်ပါ။ ကော်ပီ

Littafi Mai Tsarki

39 Ɗaya daga cikinsu ya tafi saura don ya samo ganyayen ci. Sai ya ga yaɗon inabin jeji, ya ɗebo 'ya'yan ya rungumo cike da hannu, ya zo ya yanyanka ya zuba a tukunyar abinci, ba tare da sanin ko mene ne ba.

အခန်းကိုကြည့်ပါ။ ကော်ပီ




2 Sarakuna 4:39
9 ပူးပေါင်းရင်းမြစ်များ  

Ku lura fa kada wani yă kāsa samun alherin Allah, kada kuma wani tushen ɗacin rai yă tsira har yă kawo rikici, yă kuma ƙazantar da mutane da yawa.


Ya amsa ya ce, “Duk tsiron da Ubana na sama bai shuka ba, za a tumɓuke shi daga saiwoyi.


Na shuka ka kamar zaɓaɓɓen inabi iri mai kyau da kuma wanda za a dogara a kai. Yaya kuma ka juya kana gāba da ni ka lalace, ka zama inabin jeji?


Me kuma ya rage da za a yi wa gonar inabina fiye da abin da na yi mata? Da na nemi inabi masu kyau, me ya sa ta ba da munana ’ya’ya?


Wata rana sa’ad da Yaƙub yana dafa fate. Isuwa ya shigo daga jeji, da yunwa sosai.


An yi wa katakan itacen al’ul na cikin haikalin zāne mai fasalin gora da na buɗaɗɗun furanni. An rufe bangon ciki duka da itacen al’ul, har ba a ganin duwatsun ginin.


Sai Elisha ya koma Gilgal, a can kuwa ana yunwa a yankin. Yayinda ƙungiyar annabawa suke tattaunawa da shi, sai ya ce wa Gehazi bawansa, “Ka sa babban tukunya a wuta, ka yi wa mutanen nan fate.”


Sai aka zuba wa mutanen faten, amma da suka fara ci, sai suka yi ihu suna cewa, “Ya mutumin Allah, akwai dafi a cikin tukunyan nan!” Suka kuwa kāsa ci.


Ba shi da kyau ka kasance da niyya babu sani, ko ka kasance mai garaje ka ɓace hanya.


ကြှနျုပျတို့နောကျလိုကျပါ:

ကြော်ငြာတွေ


ကြော်ငြာတွေ