Biblia Todo Logo
အွန်လိုင်း သမ္မာကျမ်းစာ

- ကြော်ငြာတွေ -




2 Sarakuna 25:4 - Sabon Rai Don Kowa 2020

4 Sai aka huda katanga sa’an nan dukan sojoji suka tsere da dare a ƙofa tsakanin katanga biyu da suke kusa da lambun sarki, ko da yake Babiloniyawa sun kewaye birnin. Suka tsere suka nufi Araba.

အခန်းကိုကြည့်ပါ။ ကော်ပီ

Littafi Mai Tsarki

4 Sai aka huda garun birnin, sarki da mayaƙa suka tsere da dare ta hanyar ƙofar da take tsakanin bango biyu kusa da gonar sarki, suka bi ta hanyar Araba, ko da yake Kaldiyawa suna kewaye da birnin.

အခန်းကိုကြည့်ပါ။ ကော်ပီ




2 Sarakuna 25:4
26 ပူးပေါင်းရင်းမြစ်များ  

A shekara ta goma sha biyu ta zaman bautanmu, a wata na goma a rana ta biyar, wani mutumin da ya gudu daga Urushalima ya zo wurina ya ce, “Birnin ya fāɗi!”


“Sarkin da yake a cikinsu zai ɗauki kayansa ya saɓa a kafaɗarsa da dare ya tafi, za a huda masa rami a katanga ya fita. Zai rufe fuskarsa don kada yă ga ƙasar.


“Ku ratsa cikin gonakin inabinta ku cinye su, amma kada ku hallaka su gaba ɗaya. Ku kakkaɓe rassanta, gama waɗannan mutane ba na Ubangiji ba ne.


Shallum ɗan Kol-Hoze mai mulkin Mizfa ne ya yi gyare-gyaren Ƙofar Maɓuɓɓuga. Ya sāke gina ta, ya yi mata jinƙa yana sa ƙofofinta, da sakatunta, da kuma sandunan ƙarfenta a wurarensu. Ya kuma gyara katangar tafkin Silowam, ta Lambun Sarki, har zuwa matakalan da suka gangara daga Birnin Dawuda.


Amma sojojin Babiloniyawa suka bi sarki, suka cin masa a filayen Yeriko. Dukan sojojinsa kuwa suka rabu da shi suka watse.


Yaya mutum guda zai kore dubu, mutum biyu su sa dubu goma su gudu, sai ko Dutsensu ya sayar da su, sai ko Ubangiji ya bashe su.


Ubangiji zai sa a rinjaye ku a gaban abokan gābanku. Ta hanya guda za ku auka musu, amma ta hanyoyi bakwai za ku gudu daga gabansu. Za ku zama abin ƙi ga dukan mulkokin duniya.


“ ‘Ga waɗanda za su ragu kuwa, zan cika zukatansu da tsoro a ƙasashen abokan gābansu har motsin ganyen da iska ta hura zai sa su ruga da gudu. Za su yi gudu kamar suna gudu daga takobi ne, za su kuma fāɗi, ko da yake babu wanda yake korinsu.


Zan yi gāba da ku har abokan gābanku su ci ku a yaƙi, su waɗanda suke ƙinku za su yi mulki a kanku, za ku gudu ba tare da wani yana korinku ba.


Sai suka yi aiki tuƙuru suna gyaran dukan sassan katangar da suka fāɗi, suna kuma gina hasumiya a kai. Ya gina wata katanga a waje da wannan, ya kuma ƙara ƙarfin madogaran gini na Birnin Dawuda. Ya yi makamai masu yawa da kuma garkuwoyi.


Kuka gina matarar ruwa tsakanin katanga biyu saboda ruwan Tsohon Tafki, amma ba ku yi la’akari da Wannan da ya yi su ba, ko ku kula da Wannan da ya shirya shi tuntuni.


Sun kewaye ta kamar masu gadin fili, domin ta yi mini tawaye,’ ” in ji Ubangiji.


Da jin motsin mahayan dawakai da maharba kowane gari ya ruga da gudu. Waɗansu suka shiga kurmi; waɗansu suka hau cikin duwatsu. Dukan garuruwan sun fashe tas; babu wani da yake zama a ciki.


Zedekiya sarkin Yahuda ba zai kuɓuta daga hannuwan Babiloniyawa ba amma tabbatacce za a ba da shi ga sarkin Babilon, zai kuwa yi masa magana fuska da fuska ya kuma gan shi da idanunsa.


Ba za ka tsere daga hannunsa ba amma tabbatacce za a kama ka a kuma ba da kai gare shi. Za ka ga sarkin Babilon da idanunka, zai kuwa yi magana da kai fuska da fuska. Za ka kuwa tafi Babilon.


Amma in ba ka miƙa wuya ga hafsoshin sarkin Babilon ba, za a ba da wannan birni ga Babiloniyawa za su kuma cinna mata wuta; kai kanka ba za ka tsira daga hannuwansu ba.’ ”


Ga abin da Ubangiji yana cewa, ‘Zan bayar da Fir’auna Hofra sarkin Masar ga abokan gābansa waɗanda suke neman ransa, kamar yadda na ba da Zedekiya sarkin Yahuda ga Nebukadnezzar sarkin Babilon, abokin gāban da ya nemi ransa.’ ”


Bayan wahala da baƙin ciki, Yahuda ta tafi bauta. Ta zauna a cikin ƙasashe, ba tă samu wurin hutawa ba. Duk masu fafararta sun same ta sa’ad da take cikin matuƙar ɓacin rai.


Diyar Sihiyona ba ta da sauran daraja. ’Ya’yan sarakunanta sun zama kamar bareyi waɗanda suka rasa wurin kiwo; cikin rashin ƙarfi suka guje wa masu fafararsu.


Da rana, yayinda suke kallo, ka fid da kayanka da ka tattara don zuwa zaman bauta. Sa’an nan da yamma, yayinda suke kallo, ka fita kamar yadda mutane masu tafiyar zaman bauta sukan yi.


Zan warwatsa dukan waɗanda suke kewaye da shi a dukan fuskokin iska, ma’aikatansa da dukan rundunoninsa, zan fafare su da takobin da aka zāre.


Ga abin da Ubangiji Maɗaukaki ya ce, “Azumin wata na huɗu, da na watan biyar, da na watan bakwai da na watan goma za su zama lokutan farin ciki da murna da kuma bukukkuwa na murna ga Yahuda. Saboda haka sai ku ƙaunaci gaskiya da salama.”


Dukan shugabanninki sun gudu gaba ɗaya; an kama su ba tare da an yi amfani da baka ba. Dukanku da aka kama an kwashe ku ɗaurarru gaba ɗaya, kun gudu tun abokin gāba yana da nisa.


ကြှနျုပျတို့နောကျလိုကျပါ:

ကြော်ငြာတွေ


ကြော်ငြာတွေ