2 Sarakuna 23:12 - Sabon Rai Don Kowa 202012 Ya rushe bagadan da sarakunan Yahuda suka kafa a kan ɗakin sama kusa da ɗakin sama na Ahaz, da kuma bagadai biyu da Manasse ya gina a filaye biyu na haikalin Ubangiji. Ya kawar da su daga can, ya farfashe su, ya zubar da tarkacen a Kwarin Kidron. အခန်းကိုကြည့်ပါ။Littafi Mai Tsarki12 Ya rurrushe, ya kuma farfasa bagaden da yake bisa rufin benen Ahaz, waɗanda sarakunan Yahuza suka gina, da kuma bagaden da Manassa ya gina a farfajiya biyu ta Haikalin Ubangiji. Sai ya watsar da tokar da ƙurar a rafin Kidron. အခန်းကိုကြည့်ပါ။ |
Sai Yosiya ya umarci Hilkiya babban firist, tare da firistocin da suke taimakonsa, da masu tsaron ƙofa su kawar da dukan abubuwan da aka yi domin Ba’al, da domin Ashera, da kuma domin dukan rundunar taurari, daga haikalin Ubangiji. Ya ƙone su a bayan Urushalima a filayen Kwarin Kidron, ya kwashe tokan zuwa Betel.