Sa’an nan Hosheya ɗan Ela ya ƙulla wa Feka ɗan Remaliya maƙarƙashiya. Ya fāɗa masa ya kuma kashe shi, sa’an nan ya gāje shi a matsayin sarki a shekara ta shirin ta mulkin Yotam ɗan Uzziya.
Ɗaya daga cikin manyan fadawansa, Feka ɗan Remaliya, ya ƙulla masa maƙarƙashiya. Ɗauke da mutanen Gileyad hamsin, ya kashe Fekahiya tare da Argob da kuma Ariye a fadan sarki a Samariya. Ta haka Feka ya kashe Fekahiya ya kuma gāje shi.
Zimri, ɗaya daga cikin shugabanni, wanda ya shugabanci rabin kekunan yaƙin Ela, ya yi maƙarƙashiya a kansa. Ela yana a Tirza a lokacin, ya bugu a gidan Arza, sarkin fada a Tirza.
Ba’asha ɗan Ahiya na gidan Issakar ya yi maƙarƙashiya gāba da shi, ya buge shi a Gibbeton, a wani garin Filistiyawa, yayinda Nadab da dukan Isra’ila suke wa garin kwanto.
Sa’ad da Ahaziya sarkin Yahuda ya ga abin da ya faru, sai ya haura hanyar Bet Haggan a guje. Yehu ya bi shi yana ihu, “A kashe shi, shi ma!” Suka ji masa rauni a keken yaƙinsa a hanya zuwa Gur, kusa da Ibileyam amma ya tsere zuwa Megiddo ya mutu a can.