Shekaru masu yawa ka yi haƙuri da su. Ta wurin Ruhunka ka gargaɗe su ta wurin annabawa. Duk da haka ba su kasa kunne ba, saboda haka ka miƙa su ga maƙwabtansu.
“Amma suka yi rashin biyayya suka kuma yi tawaye gare ka; suka sa dokarka a bayansu. Suka kashe annabawanka waɗanda suka gargaɗe su don su mai da su gare ka; suka aikata saɓo mai bantsoro.
“Manasse, sarkin Yahuda ya aikata waɗannan ƙazantattun zunubai. Ya aikata mugunta fiye da ta Amoriyawan da suka riga shi, ya kuma sa Yahuda ta bauɗe ta wurin yin zunubi saboda gumakansa.
Ubangiji ya yi wa Isra’ila da Yahuda kashedi ta bakin dukan annabawansa da kuma masu duba, cewa, “Ku juyo daga mugayen ayyukanku. Ku yi biyayya da umarnai da farillaina, bisa ga dukan Dokar da na dokaci kakanninku su bi, waɗanda na kuma bayar ta wurin bayina, annabawa.”