Amma sa’ad da kake addu’a, sai ka shiga ɗakinka, ka rufe ƙofa, ka yi addu’a ga Ubanka wanda ba a gani. Ubanka kuwa mai ganin abin da ake yi a ɓoye, zai sāka maka.
Ka ji roƙon bawanka da kuma na mutanenka Isra’ila sa’ad da suka yi addu’a, suka fuskanci wannan wuri. Ka ji daga sama, mazauninka, kuma sa’ad da ka ji, ka gafarta.
A kwanakin nan sai Hezekiya ya kamu da rashin lafiya har ya kusa mutuwa. Sai annabi Ishaya ɗan Amoz ya zo wurinsa ya ce, “Ga abin da Ubangiji ya ce, ka kintsa gidanka domin za ka mutu, ba za ka warke ba.”
“Ya Ubangiji, ka tuna yadda na yi tafiya a gabanka da aminci da zuciya ɗaya, na kuma aikata abin da yake daidai a gabanka.” Sai Hezekiya ya yi kuka mai zafi.