Sai ya tafi maɓulɓular ruwan yana watsa gishirin a ciki, yana cewa, “Ga abin da Ubangiji ya ce, ‘Na warkar da ruwan nan. Ba zai ƙara jawo mutuwa, ko yă hana ƙasar ba da amfani ba.’ ”
Daga nan sai Elisha ya tafi Betel. Yayinda yake tafiya a hanya, sai waɗansu matasa suka fito daga cikin gari, suka yi masa dariya suna cewa, “Ka haura, ya kai mai kai marar gashi! Ka haura, kai mai kai marar gashi!”