2 Sarakuna 2:14 - Sabon Rai Don Kowa 202014 Sa’an nan Elisha ya ɗauki rigar da ta fāɗo daga Iliya ya bugi ruwan da shi. Ya ce, “Yanzu ina Ubangiji Allah na Iliya?” Da ya bugi ruwan sai ruwan ya dāre gida biyu, sai ya haye. အခန်းကိုကြည့်ပါ။Littafi Mai Tsarki14 Sai ya ɗauki alkyabban nan da ta faɗo daga wurin Iliya, ya bugi ruwan, yana cewa, “Ina Ubangiji, Allah na Iliya?” Sa'ad da ya bugi ruwan, sai ruwan ya dāre, ya rabu biyu, Elisha kuwa ya haye. အခန်းကိုကြည့်ပါ။ |
Gideyon ya ce, “Ranka yă daɗe, in Ubangiji yana tare da mu, me ya sa waɗannan abubuwa suka faru da mu? Ina dukan abubuwan al’ajabinsa waɗanda kakanninmu suka gaya mana game su sa’ad da suka ce, ‘Ashe, ba Ubangiji ne ya fitar da mu daga Masar ba?’ Amma yanzu Ubangiji ya rabu da mu ya kuma sa mu hannun Midiyawa.”