2 Sarakuna 19:6 - Sabon Rai Don Kowa 20206 Ishaya ya ce musu, “Ku faɗa wa maigidanku, in ji Ubangiji, ‘Kada abin da ka ji yă firgita ka, wato, waɗannan kalmomin da karen nan na sarkin Assuriya ya yi saɓo da su. အခန်းကိုကြည့်ပါ။Littafi Mai Tsarki6 sai ya aike da amsa, ya ce musu, “Ku faɗa wa ubangidanku, Ubangiji ya ce, ‘Kada ka ji tsoron maganganun da ka ji daga bakin barorin Sarkin Assuriya, waɗanda suka saɓe ni. အခန်းကိုကြည့်ပါ။ |
Sai sarkin Assuriya ya aika da babban shugaban sojojinsa, da shugaban dattawansa, da wakilinsa daga birnin Lakish tare da ƙungiyar sojoji masu yawa zuwa Urushalima domin su yaƙi Sarki Hezekiya. Da suka haura sai suka tsaya a wurin lambatun da yake kawo ruwa daga Tafkin Tudu, kusa da hanyar Filin Mai Wanki.